Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da yin garkuwa da wasu ‘yan mata sama da 200 dake yin gudun hijira a jihar Borno.
Jami’in tuntuba kan harkokin bada tallafi na majalisar a nan Najeriya, Mohammed Malick Fall ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar a daren jiya, Inda ya ce suna cikin jimamin abunda ya faru.
Sanarwar ta baiyana cewar ba’a san adadin ‘yan matan da aka sace ba zuwa wannan lokaci, amma dai tana kiyasin sun zarta 200.
Sa’oi 48 tun bayan garkuwa da tarin ‘yan matan da aka yi, zuwa yanzu hukumomin tsaro da kuma shugabannin siyasa a kasar nan, sunki bada tabbacin abun ya faru ko kuma akasin haka.
Wasu dangin ‘yan matan da aka sace sun fadawa jaridar Daily trust cewar , suna jin cewar an wofantar dasu, biyo bayan shurun da hukumomi suka yi, tare da yin kira ga a gare su da su yi abunda ya da ce domin kubutar masu da ‘yan uwan nasu, don kaucewa maimaita irin abunda ya faru kan ‘yan matan Chibok da aka sace a shekarar 2014.