Majalisar dattawa ta tuhumi ma’aikatar shari’a kan rashin bada cikakken bayani kan yadda aka raba bashi wasu kudade har Naira biliyan 10 da milyan dari 4 a tsakanin Alkalan kasar nan.
Tuhumar ta biyo bayan nazarin rahoton kwmaitin kula da baitul malin gwamnati na shekarar 2017 da 2018 karkashin jagorancin Sanata Matthew Urhoghide, da majalisar ta yi.
Kwamitin ya yi binciken ne ta hanyar amfani da rahoton tantance kididdigar kudi da ofishin babban mai binciken kudi na tarayya ya mika wa majalisar.