Majalisar Dattawan Kasar nan, Ta amince da gudanar da bincike nan tsanaki akan yadda ake tafiyar da al’amura a Kotun kolin kasar nan, duk kuwa da Murabus din da babban Joji na Kasa, mai shari’a Tanko Muhammad yayi daga kan matsayin.
Yan majalisar Datawan sun cimma daukar wannan mataki ne a yayin zamansu na yau, biyo bayan wani kuduri da shugaban kwamitin shari’a da Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar.
Daga nan ne majalisar dattawan ta bukaci kwamitin nan daya lalubo mafita ta karshe da za’a yi amfani da ita ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin yin nazari kan korafe-korafe-korafen da aka yi game da Masu Shari’a na kotun Koli.
Idan ba’a manta ba, A makon jiya ne Kotun Kolin ta cikin wata wasika da Alkalanta suka rubuta suka yi korafin rashin samun muwalati na gudanar da aiki a Kotun kolin.