Kowane lokaci daga yanzu, Ana saran Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, zai bayyana sunayen wadanda ake son nadawa kan matsayin ministoci a zauren majalisar dattawa a cikin wannan mako da muka shiga.
Yanzu haka dai ana cigaba da tofa albarkacin baki kan jinkirin da shugaba Bola Tinubu ya yi wajen kafa majalisar ministocinsa kimanin watanni biyu bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa.
Kazalika kundin tsarin mulkin kasa ya umurci shugaban kasa da gwamnoni su kaddamar da majalisar zartarwarsu a cikin kwanaki 60 na farko a kan karagar mulki.
Sai dai wasu majiyoyi daga majalisar sun shaidawa jaridar Punch cewa wasikar da ke kunshe da sunayen wadanda ake son nadawa kan matsayin ministoci ta isa wajen shugaban majalisar dattawa a makon jiya.
Majiyar ta kara da cewa an yi wasu gyare-gyare a cikin jerin sunayen mutananen, wanda hakan ya sa aka jinkirta karanta sunayen.