A halin yanzu zamu iya baku tabbacin cewar Najeriya tana da jerin ministoci guda 45 dake dakon shan rantsuwar kama aiki. A yayin da zauren majalisar dattawa ya tantace tare kuma da tabbatar da nadin mutane 45 daga cikin 48 da shugaban kasa Bola Tinubu ya aike masu da su, domin tabbatar dasu kan matsayin ministoci.
Majisalar dattawan ta tabbatar da tantancewar mutanen ne da yammacin jiya, bayan kammala tantance su da ta yi.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i da Stella Okotete daga Delta da Danladi Abubakar daga jihar Taraba, sune wadanda majalisar bata kaiga tabbatar da tantacewar ta sub a, a yayin da take dakon rahoton tantace su daga jami’an tsaro na kasa.
Wata kila mutanen ukku sai sunyi jiran tsawon wata daya, kasancewar majalisar dattawan ta dage cigaba da zamanta zuwa ranar 26 ga watan gobe, sakamakon dogon hutun data tafi.