Ma’aikatan Lantarki a karkashin Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa, NUEE, sun fitar da sanarwar wa’adin kwana 14 a shirye-shiryen tsunduma yajin aiki ga mahukuntan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO, kan kudaden fansho da ake yankewa ba tare da turawa kamfanonin Asusun Fansho ba, da sauran matsaloli.
Ma’aikatan sun yi barazanar gurgunta ayyukan kamfanin da ake rarraba lantarki idan har hukumar ta kasa yin abin da ya dace.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a cikin wata takarda ga Manajan Darakta kuma Babban Jami'in kamfanin tare da kwafi ga shugaban hukumar tsaro ta DSS da Babban Sakatare na kungiyar ma’aikatan lantarki NUEE, Joe Ajaero, sun koka da yadda KEDCO ke cigaba da bijirewa tsarin aikewa kamfanonin fansho kudaden da ake yankewa ma’aikatan tare da sauran matsaloli da suka shafi harkokin kwadago.
Idan za a iya tunawa, kwamitin da aka kafa da ke bin diddigin biyan bashin da ma’aikatan KEDCO ke bi wanda ya ba da shawarar tsarin biyan kudin a cikin watanni hudu, ya mika rahotonsa ta cikin wata takarda mai kwanan wata 21 ga Janairu na 2022, yana mai cewa A taron da aka gudanar a ranar 30 ga Maris tsakanin kungiyar da hukumar KEDCO kan jinkiri wajen aiwatar da rahoton kwamitin hukumar ta yi alkawarin fara biyan kudaden ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai abin takaici acewar ma’aikatan shugaban kamfanin na KEDCO ya ki dawowa daga Abuja a lokacin da aka rike kudaden kungiyar ma’aikatan na watanni 12, sai basussukan fansho na watanni 56 da sauran batutuwan da suka shafi ma’aikata.