On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mai neman takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC ya sanar da raba gari da jam'iyyar

Adamu Garba, mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC

Adamu Garba yace ya fice daga jam'iyyar ne sakamakon gazawar ta wajen cika alkawuran da ta daukar wa al'umar kasar nan, da kuma yadda take fifita kudi akan cancanta.

Mai neman takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jam’iyyar APC, Adamu Garba ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar mai mulki.

Bayanin ficewar sa daga jam’iyyar na kunshe a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sa, wacce kuma Arewa Radio ta samu kwapi a ranar Laraba, inda yayi bayanin cewa ya dauki wannan mataki saboda saba hanya da yace jam’iyyar ta yi.

Adamu Garba, ya zargi jam’iyyar APC da laifin yiwa ka’idojin demukradiyya karan tsaye.

Ya kuma kara da cewa, “a matsayi na na matashi, wanda yake da yakini akan makomar Najeriya kuma ya aminta da tsarin jam’iyyar a da, ba zan cigaba da kasancewa mamba a jam’iyyar siyasar dake fifita kudi akan cancanta ba”.

“Bana tunanin akwai wani matashi dake da wata kwakwarar dama a karkashin inuwar jam’iyyar APC ba, domin tuni ta sauka daga gwadaben da aka gina ta akai tun da fari”.

Ya kuma da cewa, bugu da kari, jam’iyyar ta gaza wajen cika alkawuran da ta daukar al’umar kasar nan ta kowacce siga.