On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mai Martaba Sarkin Kano Ya Cika Shekara 61 a Duniya

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

A yau Lahadi ne mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yake cika shekara 61 na haihuwa a duniya.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wani sako da mai magana da yawun masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya sanyawa hannu, wacce ya aiko wa Arewa Radio da safiyar Lahadin nan.


An nada mai martaba sarki a matsayin sarki na 15 karkashin Sullubawan Fulani a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020, bisa sahalewar gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, aka kuma gudanar da bikin bada sanda da ya kafa tarihi a wannan kasa, idan aka yi la’akari da irin mashahuran mutanen da taron da tara, daga ciki da kuma wajen jihar nan.


Kafin shigar sa gidan dabo, mai martaba sarki ya fara rike sarautar Dan Majen Kano kuma hakimin karamar hukumar Dala, wacce mahaifin sa Alhaji Dakta Ado Bayero yayi masa a shekarar 1990, kafin ya daga likkafar sa zuwa sarautar Dan Buram a watan Octobar wannan shekara. 
Iya jagoranci da kuma tafikar da al’amuran jama’a hadi da yadda suke nuna kauna a gare shi ya sa mai martaba ya sake samun cigaba a shekarar 1992 inda aka nada shi Turakin Kano, sannan aka sake tabbatar da shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida a shekarar 2000.


Kafin cikar burin sa na zama makwafin Dabon Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kasance Wamban Kano a lokakcin mulkin sarki Mohammadu Sunusi ii, bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim, Allah ya kyauta makwanci.
Bayan canjin da aka samu na kafa Karin sabbin masarautu, jijjigen addinin ya zamo sarkin masarautar Bichi na farko a tarihi kafin sake cikar burin sa a matsayin Sarkin Kano a shekarar 2020.


A madadin shugabancin wannan gida da ma daukacin ma’aikatan ta, muna taya mai martaba sarki murna tare da fatan Allah ya inganta lafiya, ya sa rakiya ta yi nisa.