Mai horas da tawagar Super Eagles tan an gida Najeriya Jose Peseiro ya isa birnin Uyo gabanin wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika da za su kara da Sao Tome and Principe.
Peseiro wanda kwanakin baya ya amince da tsawaita kwantiraginsa ya isa birnin Uyo tare da mataimakansa a ranar Talata.
Najeriya za ta kara da Sao Tome and Principe ranar Lahadi a filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo.
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika ta nada alkalin wasa Lahlou Benbraham dan kasar Algeria a matsayin wanda zai busa wasan.