Tsohon Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele, ya sanya biliyoyin Naira a asusun bankuna 593 na kasashen Amurka da Ingila da China ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa na bankin ba.
Wani jami’in bincike na musamman kan CBN da wasu ma’aikatu, Jim Obaze, ya gano cewa tsohon gwamnan na CBN ya ajiye kudi fam billiyan 543 da milliyan 482 da 213 a asusun ajiya a bankunan kasar Birtaniya kadai ba tare da izini ba.
Obaze ya mika rahotonsa na karshe ga shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba inda ya yi ikirarin cewa ya gano kudaden da Emefiele ya zuba ba tare da izini ba a wasu asusun banki guda 593 na kasashen waje a lokacin da yake rike da mukamin.
Lauyoyin Emefiele bisa jagorancin, Mathew Bukkaa, har yanzu bai mayar da martani kan wannan zargi ba yayin da jaridun Punch ta tuntube su har zuwa lokacin gabatar da rahoton a safiyar yau.