On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Bukaci 'Yan Kasa Su Sanya Najeriya Cikin Addu'ar Neman Tsari Daga Sake Fuskantar Ambaliyar Ruwa

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’oi na neman sauki daga fuskantar ambaliya da sauran Iftila’o’i a kasar.

Abubakar ya yi wannan kiran ne a yayin bikin nadi da kuma bada sandar mulki ga sarkin Katagum na 12, Alhaji Farouq Umar a garin  Azare da ke karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi.

Sarkin Musulmin wanda ya samu wakilcin mai martaba Sarkin Kano, Alhaji  Aminu Ado Bayero, ya yi nuni da cewa, duk wani Iftila’I kamar ambaliya, Allah ne ya tsara kuma akwai bukatar a karbi wannan kaddara.

Daga nan sai ya bukaci sabon Sarkin na Katagun, Alhaji Umar Farouk da ya jajirce wajen hadimtawa  al’ummarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace suna fatan mai martaba sarkin Alhaji Umar Farouk  zai jogaranci masarautar tasa bissa gaskiya da rikon Amana.

Yayin jawabin godiya Sarkin na Kano Alhaji Aminu Bayero ya godewa dukkanin manyan  bakin da suka halarci wannan taro daya gudana a masarautar katagum dake jihar Bauchi.

A nasa jawabin sabon sarkin na katagum Alhaji Umar Farouk ya godewa gwamnatin jihar bauchi bisa  karamci da dukkanin sarakunan kasar nan suka samu zuwa bikin bada sanda da gwamnan jihar bauchi Bala Abdulkadir Muhammad yayi masa.

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Mai martaba sarkin kazaure Alhaji Najib Husaini Adamu  da mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bammali da mai martaba Shehun Barno da dai sauran sarakunan  kasar nan sun halarci wajan taron.