On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Mahajjatan Najeriya Ba Zasu Sake Fuskantar Matsalolin 2022 Ba - Mutawwif/NAHCON

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON da Kamfanin kula da mahajjatan da suka fito daga nahiyar Afrika wadanda ba larabawa ba, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar ayyukan da zasu gudanar a lokacin aikin hajjin bana  2023 domin kaucewa matsalolin da suka faru a 2022.

Yarjejeniyar ta samu sanya hannun shugaban hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da kuma shugaban Kamfanin kula da mahajjatan nahiyar Afrika wadanda ba larabawa ba Ahmad Sindy.

Wata sanarwa da hukumar ta NAHCON ta fitar mai dauke da sahannun mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar Musa Ubandawaki, ta nuna cewa yarjejeniyar ta kunshi yadda Kamfanin zai kyautata tsarin hidima da ciyar da mahajjatan, tare da ragin kaso biyar cikin dari na kuɗaɗen da za'a biya na hidimar a wannan shekara.

A jawabinsa tun da farko shugaban hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana rashin jin dadi game al'amarin da ya faru a shekarar da ta gabata kan wahalhalun da Alhazan Najeriya suka fuskanta daga ayyukan kamfanonin kula da mahajjatan, wanda yace ba ya fatan hakan ta sake faruwa, hakan ce kuma ta sanya su ƙulla wannan yarjejeniya domin sanin matsayar kamfanonin da kuma hidimar da zasu yi.

A lokacin da yake gabatar da tsare tsaren da suka shirya shugaban Kamfanin kula da mahajjatan a ƙasar Saudiya Ahmad Sindy, ya sha alwashin cewa matsalar da Alhazan Najeriya suka fuskanta a shekarar da ta gabata ba zata sake faruwa ba, sakamakon zage damtse da suka yi, wajen inganta ayyukan nasu a wannan shekara, domin saukakawa mahajjata da kuma samar musu da walwala da jin dadi.

Aikin hajjin wannan shekara ta 2023 ana sa ran zai fara ne daga ƙarshen watan Yuni.