Ma’aikatar gona da Raya Karkara ta Tarayya, ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa cewa ta kashe Naira biliyan 18 da milliyan 9 wajen aikin sarewa da share dazuka a lokacin kulle-kullen Corona, kamar yadda kwamitin majalisar wakilai kan baitamali ya yi zargin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Gona da Raya Karkara ta Tarayya, Dokta Joel Oruche ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
A cewar ma’aikatar, kudaden da kwamitin majalisar ke zargi ya fade su ne ba tare da wani dalili ba.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, wannan batu da ake zargi ba gaskiya ba ne.