Hukumar kidaya ta kasa tace jimillar yan Najeriya milyan 1 ne zasu yi aikin kidayar da gwamnati zata gabatar a shekarar 2023.
Kazalika hukumar ta tabbatar da cewa za’a yi amfani da wata fasahar zamani wadda ake da tabbaci kanta wajen gudanar da aiki domin kawar da saka son zuciya daga bangaren yan siyasa da wasu masu fada aji da zasu iya yiwa shirin zagon kasa.
Kwamishinan hukumar mai wakiltar jihar Ekiti Mister Deji Ajayi ne ya baiyana haka yayin wani taron manema Labarai da aka gabatar a jiya.
Da yake jawabi game da muhimmancin da kidayar ke dashi ta bangaren gina kasa da kuma amfani dashi wajen daukar matasa aikin yi.