Kungiyoyin ma’aikatan sufurin jiragen sama sun dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon ganawar da suka yi tsakaninsu da jami’an ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa.
Kungiyoyin sun baiyana matakin nasu ne ta cikin wata wata sanarwa da aka fitar a birnin taraiyya Abuja.
Sanarwar ta baiyana cewar kungiyoyin sunyi la’akari ne da abunda zai zama masalaha ga bangaren sufurin jiragen sama a kasar nan, A yayin da zasu yi dakon matakin da gwamnatin taraiyya zata dauka a yayin ganawar da zasu yi ranar 9 ga watan nan na Mayu.
Janye shirin tafiya yajin aikin na zuwa ne , kasa da mako daya bayan da kungiyoyin sufurin jiragen sama suka yi barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon matsalolin da suka danganci biyansu albashi da rashin kyawun yanayin gudanar da aiyuka a tsakanin ‘ya’yansu.