On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ma'aikatan Najeriya Ku Sha Kuriminku Sabon Mafi Karancin Albashi Na Nan Tafe - Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi tsumin kudi Naira trilliyan 1 cikin watanni biyu da cire tallafin man fetur.

A jawabinsa ga ‘yan kasa a daren jiya, Tinubu ya ce a wadannan kudade wadanda da an  kyalesu da tuni sun salwanta, yanzu za’ayi amfani da  su a cikin shirye-shiryen tallafawa iyalai a fadin kasarnan.

Yayin da yake tabbatar da  wahalhalun da ba za a iya kaucewa ba a cikin matakan da gwamnatinsa ke dauka a cikin kwanaki 62 da suka gabata, shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya suyi tunanin gobensu tare da yakinin samun makoma mai kyau a nan gaba.

Shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin bullo da sabon mafi karancin albashin ma’aikata da kuma fitar da al’ummar kasa daga cikin tabarbarewar tattalin arziki.