Mambobin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya sun bayyana aniyarsu ta tsunduma yajin aikin a duk fadin kasarnan daga gobe Laraba idan har ba a biya musu bukatunsu ba sakamakon cikar wa’adin kwanaki 21 da suka bayar a watan Satumba.
Kungiyar ta bukaci, gwamnonin jihohi su fara aiwatar da ikon cin gashin kai ga majalissa wajen harkokin kudi cikin gaggawa kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
A wasikar sanarwa da aka rubutawa shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya da shugaban kungiyar shugabannin majalissun dokokin jahohi da hukumar tsaron farin kaya, ma’aikatan sun bayyana cewa tun da farko sun bayar da wa’adin kwanaki 21 gabanin tafiya yajin aiki da zai fara daga gobe.
Wasikar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta na kasa, Mohammed Usman, ta nanata shirin kungiyar na umurtar mambobinta da su shiga yajin aikin idan har bukatar bata biya ba.