
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Benue, Terungwa Igbe, ya bukaci gwamnatin jihar da ta temaka ta biya dukkanin wasu basussukan albashin ma’aikata da kuma na fansho da ake binta.
Igbe, wanda ya koka kan halin da ma’aikata ke ciki a jihar, ya yi wannan kiran ne a sakatariyar jihar da ke kan titin Otukpo maimakon dandalin taro na IBB, wurin da ma’aikata suka saba gudanar da bikin ranar ma’aikata a kowace shekara.
Ya ce ma’aikatan sun zabi gudanar da bukukuwan ne batare da yin gagarumin wasu taruka ba, saboda basussukan albashi da ake bin gwamnatin jihar.
Shugaban kungiyar ta NLC ya kuma bukaci a mayar da shekarun ritayar ma’aikata daga shekara 35 zuwa shekara 40, da kuma cika shekaru 65 a matsayin na ritaya a maimakon shekaru 60 da ake yi a yanzu.