A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gudanar da bukin ranar ma’aikata ta karshe a matsayinsa na shugaban kasa a yau, kungiyoyin kwadago sun baiyana kwazon gwamnati mai ci tare da gwamnatocin jihohi a matsayin wanda ba yabo ba fallasa,Suna masu baiyana cewar ‘yan Najeriya sunsha fama da matsala ta tsadar rayuwa.
Da yake magana dangane da ranar Ma’aikata, Ma’ajin kungiyar kwadago ta NLC Hakeem Ambali, Ya ce gwamnati mai ci ta jefa ma’aikatan kasar nan cikin kunchin rayuwa da wahalhalu iri-iri.
Ya kara da cewar wasu ma’aikatan sun rasa aikinsu a yayin da matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa da sauran wasu matsaloli a karkashin gwamnatin Buhari suka jefa jama’a da dama cikin kangin rayuwa.
To sai dai kuma a martanin da fadar shugaban kasa ta yi, Ta jaddada cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka rawar azo a gani kan samun cigaban kasar nan, duk kuwa tarin sukar da yake fuskanta, Tana mai cewar zai sauka mulkin kasar nan ne ba kamar lokacin da same ta tana cikin wanayi na ban tausayi ba.
Wata sanarwa da tawagar masu kula da harkokin sadarwa na fadar shugaban kasa suka fitar mai dauke da shafuka 91 a ranar Lahadi, Sun baiyana irin dimbin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa muhammadu Buhari ta samu a cikin shekara Takwas da yayi yana mulkin kasar nan, inda suka yi bayani kan wasu bangarori har guda 20.
Sanarwar mai dauke dasa hannun kakakin shugaban kasa, Femi Adesina , Ta baiyana cewar shugaban kasar ya zama tamkar wanda ya tsamo kitse daga wuta kan halin da ya samu kasar nan.