Wata kungiya mai zaman kanta a Kano kan tsaro da cigaban al'umma ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta duba halin da ma’aikata su dubu 10 da dari 8 da aka dakatar ke ciki.
Shugaban kungiyar ta KSDF, Comrade A A Haruna Ayagi ne ya yi wannan kiran yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Kano.
Ya tunatar da gwamnati cewa ma’aikatan da abin ya shafa suna cikin mawuyacin hali a sakamakon wannan mataki na dakatar da albashinsu.
Ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba akan al-amarin akan lokaci, domin amfanin jihar Kano da al-umarta.
Ya shawarci gwamnatin jihar da ta yi tunani ta inganta zamantakewar tattalin arzikin al'ummarta maimakon kallon batutuwan da gwamnatin da ta shude ta aiwatar ta hanyar doka da tsarin mulki.
"Babban burinmu shi ne mu tabbatar da cewa Kano ta ci gaba a kowane fanni na siyasa, tattalin arziki da zamantakewa, maido da abubuwan da suka faru a baya, zai iya haifar da dagula zaman lafiya da tsaro da zaman lafiyar jihar." Acewar Ayagi.
Shugaban kungiyar, Ayagi, ya ci gaba da yin kira ga gwamnatin Kano da ta guji daukar wani mataki a kan batutuwan da ke gaban kotu.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta mutunta alfarmar kotun a matsayin wurin samun adalci na karshe ga talaka, yayinda dokar kasa ba ta ba da damar yin tsokaci ko tsoma baki kan duk wata matsala da ke gaban kotu ba.
Daga nan sai ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda domin samun ci gaban jihar Kano.
Ya kara da cewa KSDF kungiya ce cikin kungiyoyi masu zaman kansu da aka kafa don taimakawa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro don samun bayanan sirri don inganta zaman lafiya da hadin kai.