Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado ba zai amince da sabon kudirin karawa ma’ikata shekarun Ritaya zuwa shekaru 65 ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin.
Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, ta bakin shugabanta na kasa, Joe Ajaero, ta nemi da a karawa ma’aikatan gwamnati sabuwar shekara ta ritaya a lokacin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2023 a Abuja.
Sai dai Keyamo, ya ce gwamnati maizuwa ce kawai zata iya kara shekarun..
Ministan ya bayyana cewa ba za a iya kammala aikin ba kafin karshen wa’adin mulkin Buhari. Don haka yace yana tsammanin sabuwar gwamnati za ta yi hakan.