Dillalan Man fetir sunyi hasashen cewar farashin litar man fetir zata iya haura naira 700 a nan jihar Kano da wasu jihohin Arewacin kasar nan, daga wata mai kamawa na Yuli.
Shugaban kungiyar dilallan man fetir ta kasa masu zaman kansu, IPMAN, Mike Osatuyi, Ya fadawa manema Labarai cewar, Farashin litar man fetir zata iya haura naira 700 a yankin arewacin kasar nan, da zarar ‘yan kasuwar mai sun fara dauko sabon man fetir a wata mai kamawa.
Ya kara da cewar mutanen dake zaune a yankin Arewacin kasar nan zasu rika biyan sama da naira 700 kan kowace litar man fetir, Yayin da wadanda suke a wajen jihar Legas, zasu rika sayen litar man fetir din sama da naira 610, sai kuma wadanda suke zaune a cikin birnin Ikko, da zasu rika sayen litar man fetir din kan naira 600.