Farashin man fetur ya karu zuwa Naira Dubu 1 da 200 kan kowace lita a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a jiya, Tun bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiyana cire tallafin mai.
Wani mazaunin birnin mai suna, Darlington Okeke, ya danganta matsalar da yawan siyan man da jama’a ke yi, sakamakon shiga yanayin razana kan yuyuwar samun karancin man, tun bayan furucin da Tinubun ya yi a ranar Litinin.
Hakazalika farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 600 a kan kowace lita a mafi akasarin sassan kasar nan, lamarin da ya sa aka samu tashin kudin sufuri da kimanin kaso 100 bisa 100.
Dogayen layukan dai sun sake kunno kai a gidajen mai a jihohin Legas da Abuja sai Ilorin da Benin da birnin Asaba da birnin Fatakwal sai nan jihar Kano da birnin Makurdi da sauran manyan biranen dake kasar nan.