Kungiyar manyan ma’aikatan mai da kuma iskar gas ta kasa PENGASSAN,Ta ce za’a rika siyar da litar man fetir tsakanin naira 360 zuwa 400 bayan janye tallafin man fetir da gwamnati ke biya.
Shugaban kungiyar na kasa,Festus Osifo ne ya baiyana haka ga manema Labarai a jiya, a gefen taron kolin kungiyar da aka shirya a Abuja babban birnin taraiyya.
Sai dai kuma ya ce kungiyar ta umarci daukacin mambobinta dake fadin kasa dasu tabbatar sun samar da wadataccen mai ga yan Najeriya,tare da yin barazanar kwace lasisin duk wani dan kungiyar da aka samu yana boye man fetir.