Kungiyar likitoci ta kasa masu zaman kansu ta kalubalanci yunkurin majalisar wakilai ta kasa na wajabta yin aikin tsawon shekara biyar a Najeriya ga duk wani Likita mai lasisi dake kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa,Dr Kayode Adesola ne ya baiyana haka yayin hirarsa da manema Labarai a birnin Ikko, Ya ce yunkurin aiwatar da kudin dokar an yita ba bisa tsari ba, wanda zauren majalisar ke tunanin yin haka zai magane matsalar ficewar likitoci zuwa kasashen waje.
Ya kara da cewar yadda aka gabatar da kudurin dokar,Ya nuna cewar ba’a yi wani kyakykyawan nazari da bincike ko kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin domin jin ta bakinsu kan illolin dake tattare da yin hakan.
Ya kuma kara da cewar Likitocin kasar basa bukatar samun wani Lasisi daga Najeriya domin samun damar yin aiki a wasu kasashe,A saboda haka sai ya yi kira da ‘a saka dokar ta baci a bangaren kiwon lafiya na kasar nan, domin magance tarin kalubalen dake damun bangaren.