Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta kasa ta aiyana tafiya yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon kin biyanta hakkokinta na alawus da kuma sauran wasu bukatu.
Shugaban kungiyar na kasa, Dr. Orji Emeka Innocent, shi ne ya bada sanarwar shiga yajin aikin a daren jiya, jim kadan bayan kammala zaman kolin kungiyar a Legas.
Ya ce zasu fara yajin aikin ne da tsakar daren yau, Inda ya baiyana bukatun da suke neman gwamnati ta biya masu, wanda ya hada da biyansu alawus na daukar horo.
Sauran bukatun sun hada kudaden ariyas da kuma sake yin nazari kan tsarin biyansu albashi da dai sauransu.