Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta baiyana cewar duk da sabon matsayar da gwamnatin taraiyya ta dauka, kan kudirin dokar wajabta yin aikin shekara biyar a kasar nan kafin Likita ya samu lasisin aiki, Hakan ba zai hana ta shiga yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyar ba.
Shugaban kungiyar na kasa, Dr Innocent Orji ne ya baiyana haka lokacin da yake ganawa da manema Labarai , kan abubuwan da suka tattauna a yayin taron kolin kungiyar na kasa.
Ya ce zasu fara yajin aikin ne tun daga karfe 8 na safiyar ranar Laraba. Wasu alamu dai na nuni da cewar ba iya kudirin dokar kadai bane,abunda yake damun likitocin masu neman kwarewa.
A ranar 29 ga watan Aprilun bana ne kungiyar ta fitar da sanarwar jan kunne, tare da baiwa gwamnatin taraiyya wa’adin makwanni biyu, data aiwatar da karin albashin likitoci na bai daya, CONMESS ko kuma ta fuskanci tafiya yajin aiki.