On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Fitar Da Sabon Wa'adi Ga Gwamnatin Najeriya

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta baiwa gwamnatin tarayya sabon wa'adin mako biyu kan aiwatar da karin kashi 200 na albashin mambobin kungiyar.

Likitocin  sun cimma wannan matsaya ne a ranar Laraba a wani taron majalisar zartarwa na kungiyar na kasa  na musamman don tantance matakin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta sanya wa hannu a ranar 19 ga Mayu, 2023 bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.

Likitocin, a cikin sanarwar, sun yi kira ga gwamnati da ta biya dukkan basukan mambobinta ba tare da bata lokaci ba, da suka hada da alawus alawus din hadari da kuma bashin  shekarar 2014 zuwa 2016.

Sanarwar ta kara da cewa Likitocin ba za su iya ba da tabbacin cigaba da kula fannin Lafiya ba idan duk bukatunsu basu biya ba a karshen wa'adin ranar 19 ga Yuli 2023.