kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta koka kan yadda matsalar Likitoci dake tafiya kasashen waje aiki ke shafar bangaren kiwon lafiya a jihar kano, inda ta ce likitoci 533 ne kawai ke karbar albashin gwamnatin jihar Kano a yanzu haka.
Shugaban Kungiyar na jihar Kano, Dr. Abdullahi Kabir Sulaiman, shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a nan birnin Kano, inda ya dora alhakin matsalar kan rashin kyawun aiki da albashin mai inganci ga ma’aikatan lafiya.
Sulaiman ya ce likitoci da dama sun bar aikin gwamnati a matakin jihar kano inda suka koma yin ayyuka a asibitocin gwamnatin tarayya da sauran jihohin da ke da ingantattun kayan aiki da kuma albashi mai inganci.
A saboda haka ya shawarci gwamnatin jihar Kano da ta magance matsalar banbancin albashin ma’aikatan lafiya da ake samu tsakanin ma’aikatan lafiya na jiha da na tarayya domin magance matsalar ficewar likitoci da ake samu zuwa kasashen waje domin yin aiki.