Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi karin mako guda a birnin Landan, bisa bukatar da likitansa na Hakori ya nema,sakamakon duba shi da ya fara yi.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, shi ne ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a daren jiya.
Adesina ya ce kwararren likitan na bukatar ganin shugaban kasar nan da wasu kwanaki biyar domin duba lafiyar hakoransa.
Idan ba’a manta ba Shugaba Buhari ya bi sahun sauran shugabannin duniya wajemn halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na ukku a ranar 6 ga watan Mayun da muke ciki.