Shugabancin jam’iyyar Labour na kasa tsagin Lamidi Apapa, Ya musanta karbar naira milyan 500 daga hannun wani mutum, domin wargaza karar da jam’iyyar ta shigar a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa.
Da yake yiwa manema Labarai jawabi, Jim kadan bayan ya tsallake rijiya da baya daga wasu matasa da suka rika yi masa Ihu jiya a Abuja, Lamidi Apapa, Ya musanta karbar wasu kudi daga hannun wani ko wata kungiya domin yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Ya kara da cewar ya zama wajibi, Peter Obi ya zama bashi da wani bangare, domin warware rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar a matakin kasa.
Kazalika ya baiyana ihun da matasan suka yi masa a gaban kotun kuma a gaban Peter Obi, a matsayin kaskanci da kuma wani salo na irin nagartar shugabancin da Obi ke dashi.