Har yanzu babu wata alamar tsayawa a yakin da ake gwabzawa a zirin Gaza sakamakon cigaba tashin bama-bamai da kuma harba makaman roka da ake yi.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a yau kan matsalar gudanar da aiyukan jin kai a yankin, bayan da Isra'ila ta fadada kai hari Falasdinu a karshen mako.
A yayin taron wanda Hadaddiyar Daular Larabawa ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar zai tattauna kan matsalolin gudanar da aiyukan jin kai a falasdinu.
Ya zuwa yanzu dai kwamitin sulhun ya gaza daukar wani mataki a yunkurin da aka yi na tsagaita wuta har sau hudu, tun bayan da kasashen Rasha da Amurika suka hau kujerar na’ki.