
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini, ya ba da umarnin kamo wani mai matashi mai suna Ibrahim Musa dan shekaru 22 a duniya , wanda ake zargin ya halaka mahaifiyarsa mai suna Hajara Mohammed mai shekaru 50 a duniya, Ta hanyar daba mata wuka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa shi ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a nan Kano.
Ya kara da cewa, An garzaya da matar zuwa Asibitin koyarwa na Mohammed Abdullahi Wase da ke nan Kano, inda a nan ne kuma wani Likita ya tabbatar da mutuwar ta.
Ya kuma baiyana cewar an samu wata wuka dauke da jini a jikinta wadda ake zargin da ita matashin ya yi amfani wajen aikata danyen aikin.
Kakakin rundunar yansandan jihar Kano ya ce a yanzu haka kwararrun jami’ansu na kan neman matashin ruwa a jallo.