Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ayuba Elkanah ya yi ritaya bayan ya shafe shekara 32 yana aikin dan sanda.
Elkanah ya bayyana haka ne a wajen wata liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a ranar Alhamis a Gusau babban birnin jihar zamfara, yace bai yi nadamar shiga aikin ‘yan sanda ba.
Ya kuma yabawa babban Sufeto Janar na ‘yan sandan kasarnan Usman-Baba Alkali da gwamnan jihar Bello Matawalle, da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da jami’ai da jami’an rundunar bisa goyon bayan da suka baayar, wanda ya haifar da nasarori daban-daban.
A nasa jawabin, gwamna Bello Matawalle, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Hassan Nasiha ya taya Elkanah murna, ya kuma ce jihar Zamfara za ta rasa wani ginshiki mai karfi wajen yaki da matsalar tsaro.