Wata kungiyar farar hula, mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bukaci rundunar 'yan sandan kasa da kasa da sauran hukumomin da abin ya shafa da su sanya tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano cikin jerin sunayen wadanda ake sa Ido akansu kan badakalar bidiyon dala.
Jagoran kungiyar, Comrade Kabiru Saidu Dakata ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Kano, inda ya ce Ganduje zai iya ficewa daga kasarnan ba da dadewa ba.
Dakata ya zargi Ganduje da yin amfani da umarnin kotu a matsayin dabarun jinkiri wajen yin zagon kasa ga binciken faifan bidiyo na Dala, yayinda abokansa na siyasa ke takama da cewa Ganduje nada goyon bayan fadar shugaban kasa.INSERT....
Ya ce kamata ya yi gwamnatin da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta ta kare martabarta ta hanyar kammala binciken Ganduje domin kaucewa kafa hujjar cewa Najeriya nada kantar cin hanci da rashawa.