On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyoyin Kwadago Sunyi Barazanar Kauracewa Ganawarsu Da Gwamnatin Tarayya

YAN KWADAGO

Kungiyar kwadago ta yi barazanar ‘kauracewa ganawar da aka shirya yi tsakaninta da gwamnatin tarayya a yau Litinin 30 ga watan Octoban da muke ciki, Matukar ministan kwadago Simon Lalong ya halarci tattaunawar.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Joe  Ajaero ne ya yayi wannan barazana a yayin da yake amsa tambayoyin manema Labarai a Abuja, Inda  yake  masu kari haske  kan halin da ma’aikata suka tsinci kansu  ciki a jihar Imo.

Kwamared Ajaero  ya soki ministan kwadagon  saboda  rashin iya ‘kulla  kyakykyawar alaka  tsakaninsa  da gamaiyyar kungiyoyin kwadago.

Ya kuma yi gargadin cewar zai tattaro kan ‘ya’yan kungiyar  domin yiwa jihar Imo  tsinke a ranar Laraba mai zuwa  1 ga watan Nuwamba,  sakamakon zargin gwamnatin jihar da take  ‘yacin ma’aikata a jihar.