Gamaiyyar kungiyoyin kwadago a kasar nan sunga baiken gwamnatin tarayya kan rashin cigaba a biyan ma’aikata karin albashi na wucin gadi na naira dubu 35 da aka yi masu, sakamakon janye tallafin mai da aka yi.
A jiya ne ma’aikatan gwamnatin tarayya suka tabbatar da cewar, gwamnatin ta yi masu karin naira dubu 35 ne sau daya kadai a albashinsu na watan Satumba, sabanin alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi, na cewar za’a cigaba da basu karin har zuwa lokacin za’a bullo da sabon tsarin biyan albashi mafi kankanta.
Shugaban sashin yada labarai na kungiyar kwadago ta kasa, Benson Upah ya baiyana matakin a matsayin na yaudara wanda kuma ba zasu lamunta ba, inda y ace kungiyar zata dauki mataki batare da bata lokaci ba.
To sai dai kakakin ofishin babban akanta na kasa, Bawa Mokwa ya kawar da fargabar da ma’aikatan suka nuna, inda ya ce a yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin tabbatar da ma’aikatan sun karbi karbin albashin na wucin gadi da aka yi masu.