Shugabancin gamaiyyar kungiyar kwadago ta kasa ya janye yajin aikin sai Baba ta gani da kungiyar ta fara a fadin kasa daga ranar Talatar data gabata, a wani mataki na nuna borenta kan cin zarafin da aka yiwa shugaban kungiyar kwadago na kasa NLC, Kwamared Joe Ajaero a jihar Imo.
A daren jiya ne kungiyar ta sanar da janye yajin aikin bayan wata ganawa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Wanda ya tabbatar da cewar an kama mutane biyu da ake da zargi da cin zalin shugaban kungiyar kwadagon na kasa, tare da rokonsu dasu janye yajin aikin.
Babban sakataren gamaiyyar kungiyoyin ma’aikata ta kasa, Kwamared Sikiru Waheed ne ya tabbatar da janye yajin aikin na sai Baba ta gani ga manema Labarai.
Kwamared Waheed ya jinjinawa Ma’aikata saboda jajircewar da suka nuna wajen ganin yajin aikin ya tabbata cikin nasara, tare da umartarsu da su koma bakin aiki daga yau Alhamis.