Kungiyar kwadago ta kasa ta lashi takobin tsayar da dukkanin wasu harkoki a kasar nan cak , a yayin da zata fara yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu a fadin kasar nan daga yau, a wani mataki na nuna damuwa kan halin matsin rayuwa da jama’ar kasa suka samu kansu a ciki, tun bayan janye tallafin man fetir.
Masu ruwa da tsaki a bangaren tattalin arzikin kasa, da suka hada da Bankuna da kungiyoyin farar hula da kungiyoyin ma’aikata na goyon bayan yajin aikin da za’a soma daga yau, a kokarinsu na ganin an magance matsalolin da tattalin arzikin kasa ya samu kansa a ciki.
Ma’aikatan bankuna da kungiya kwararrun ma’aikata a bangaren gudanar da harkokin kudi sun yi alkawarin rufe wuraren aiyukansu daga yau.
Wata sanarawa da babban sakatarensu, Mohammed Sheika ya fitar, Ta tabbatar da cewar zasu shiga yajin aikin, inda suka ce akwai bukatar jawo hankalin gwamnatin tarayya kan halin da ‘yan kasa ke ciki.
Nan kuma, Shugabancin kungiyar kwadago ta kasa, NLC, Ya kauracewa taron da ministan kwadago Simon Lalong ya shirya, da zummar ganin an dakile shirin tafiya yajin aiki na tsawon kwanaki biyu da kungiyar zata fara daga Yau.
Rahotanni sun baiyana cewar shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne kadai ya halarci zaman wanda aka fara da karfe 5 da rabi da minti biyu na yammacin yau.
An yi ganawar ne cikin sirri, A yayin da ministan kwadagon ya roki yan Jarida dasu temaka su bar wajen taron, domin kyale masu ruwa da tsaki su tattauna kan muhimman abubuwan da aka sanya gaba.
A ranar juma’a data gabata ce, Kungiyar kwadagon ta aiyana tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu farawa daga ranar Talatar nan, sakamakon halin tsadar rayuwa da jama’a suke ciki.