Gamaiyyar kungiyoyin kwadagon kasar nan sun baiwa gwamnonin jihohi wa’adin makwanni biyu dasu fara yin aiki da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya na yiwa ma’aikata Karin naira dubu 35 a albashinsu.
Wannan dai na daya daga cikin alkawuran da aka kulla tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadagon.
Shugabannin kungiyoyin kwadagon a matakin jihohin wadanda suka bada wannan wa’adi a jiya Talata, Sunce sun rubutawa gwamnonin wasika kan tsare-tsaren aiwatar da Karin albashin na wucin gadi wanda za’a yi aiki da shi tun bayan janye tallafin mai.
Da yake tabbatar da daukar matakin, Shugaban kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa , Y ace sun aikewa da gwamnati jihar kano sakon nasu, kuma a yanzu suna dakon suga matakin da zata dauka, tare da fatan gwamnati zata yi abunda ya dace kafin karewar wa’adin da suka bayar.