Kungiyar kwadago ta bayyana rashin gamsuwarta da tafiyar hawainiya wajen aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da ta rattaba hannu da gwamnatin tarayya don dakile yajin aikin da ta shirya tsunduma a fadin kasarnan.
A sassan jihohin Najeriya kungiyoyin NLC da TUC sun ce rashin aiwatar da yarjejeniyar kafin wa'adin ranar 30 ga watan Oktoba na iya kaiwa ga babu wani zabi illa dakatar da ayyuka da sauran al’amuran yau da kullum a fadin Najeriya wanda tun sun fara hada kan mambobinsu a fadin kasarnan.
Da aka tambaye shi ranar Talata ko ‘yan kwadago sun gamsu da aiwatar da yarjejeniyar, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC, Benson Upah, ya ce, “A’a. Gwamnati na iya yin yunkuri mafi kyau da sauri.
Shima da yake zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar TUC na jihar Ogun, Akeem Lasisi ya bayyana cewa, aiwatar da mafi yawan yarjejeniyoyin suna kan teburin gwamnatin tarayya, inda ya kara da cewa babban abin da ya fi muhimmanci ga jahohi da kananan hukumomi shi ne biyan albashin ma’aikata.