Kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU, ta bayyana dokar bada lamunin karatu ga daliban manyan makarantu a kasar nan, da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanyawa hannu a jiya, matsayin nuna banbanci tsakanin ‘ya’yan masu hannu da shuni da kuma ‘ya’yan talakawa.
Da yake mayar da martani kan dokar da shugaban kasa ya saka wa hannu, shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce idan har da gaske an samar da dokar ne domin amfanin yaran da iyayensu ke samun samun abunda bai wuce naira dubu 500 a shekara ba, hakan na nufin daliban da iyayensu ke samun fiye da wannan kudi a shekara, ba zasu ci gajiyar tsarin ba.
Bugu da kari shima Shugaban Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Kasa, Anderson Ezeibe, ya ce abune mai wahalar gaske yadda aka dora tsarin kan cewar daliban da suka karbi bashin,su mayar da kudin bayan shekara biyu da kammala aikin hidimtawa kasa.
A cewarsa, Ba lallai ba ne daliban da suka karbi bashin su samu aikin yi a shekara biyu bayan sun kammala aikin hidimtawa kasa.