A yaune Kungiyar Malaman Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, zata sake ganawa da wakilan gwamnatin taraiyya akan dambawar yajin aikin da suke kan yi wanda yanzu haka yake cikin wata na shida da somawa.
Shugaban Kungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, Yace ganawar da zasu sake yi zata mayar da hankali ne kan yarjejeniyar da suka kulla tsakaninsu da gwamnatin taraiyya a shekarar 2009.
Kazalika yace bukatunsu basu tsaya ga iya maganar tsarin biyansu albashi ba, harma da abubuwan da suka shafi samar da sabon tsari na gudanar da jami’oi da basu damar cin gashin kansu, da kuma samar da kudaden tafiyar da jami’oin.
Sai dai kuma shugaban kungiyar jami’oin ta kasa yace gwamnatin taraiyya ta takaita bukatun nasu ga iya maganar yadda ake biyansu albashi, Yace idan har ganawar da zasu yi a yau ta haifar da ‘Da Mai Ido, To Babu shakka zasu janye yajin aikin da suke yi.