Kungiyar ‘yan kasar China mazauna Jihar Kano dake gudanar da harkokin kasuwanci tayi Allah-wadai da kisan da Geng Quanrong ya yiwa Ummukhulthum Sani Buhari, matashiya ‘yar jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da fadar wakilin mutanen China a Kano Mr. Mike Zhang ta fitar dauke da sahannun mataimakinsa na musamman, Mista Guang Lei, Zhang, ya ce kisan abun tir ne da Allah wadai, kuma wani laifi ne da ya kamata hukumomin tsaro da abin ya shafa su yi aiki akai.
A cewar sanarwar "Al'ummar China mazauna Kano suna goyon bayan dokar tayi aikinta yadda ya kamata akan al’amarin.
Har ila yau, sun yaba da irin karramawar da ake yi wa ’ya China mazauna Kano, kuma za su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, da sada zumunci da ba da gudummawa wajen ci gaban Kano.
A cikin sanarwar, al’umma ta China Mauzauna Kano ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayiyar Ummukhulthum Buhari.
Tuni gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin bin hakkin marigayiyar, ya ce ‘’wannan "Zub da jini ne, saboda haka dole ne sai doka ta yi aikinta.
Al’amarin dai ya faru ne a daren ranar Juma'a, inda Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wanda ake zargi kuma tana ci gaba da gudanar da bincike, inda ta mika al’amarin ga sashen binciken manyan laifuka.
Wannan kisa na Umiita dai ya bude sabon shafin martani a zauruka da sauran shafukan sada zumunta a ciki da wajen Najeriya.