Kungiyar Yan Jarida ta kasa ta baiyana matakin da Hukumar Kula da kafafen Yada Labarai ta kasa NBC ta dauka na soke lasisin wasu kafafen yada labarai har 52 sakamakon taurin bashin da take binsu, a matsayin wani hukunci na gaggawa wanda zai maida hannun agogo baya.
Ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Chiris Isiguzo ya fitar, Yace hukumar ta dauki matakin ne batare da yin nazari da kuma tuntuba ba, musamman la’akarin da halin rashin tsaro da kasa ke ciki.
Daga nan sai tayi kira ga hukumar NBC data yi kaffa-kaffa kan matakin la’akarin da yanayin tsaro da kasa ke ciki, tare da sake bada kofar tattaunawa domin samar da masalaha akan matsalar.
A ranar juma’a ne Hukumar kula da Kafafen Yada Labarai ta kasa ta soke lasisin kafafen yada labarai 52 cikinsu hadda gidan Talabijin na Silverbird da AIT da gidan Rediyon Raypower da sauransu skaamakon kin sabunta lasisinsu da suka kayi, wanda jimillar kudaden da take binsu zai kai naira bilyan 2 da milyan 66.