Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da Ma’aikatun gwamnati SERAP,Tayi kira ga shugaban Kasa Muhammadu daya gaggauta janye barazanar saka takunkumi akan wasu kafofin yada Labarai biyu, kamar yadda ministan yada Labarai Lai Mohammed ya baiyana.
A ranar Alhamis din data gabata ce, Ministan ya baiyana cewa gwamnatin taraiyya zata sakawa kafar yada labarai ta BBC da kuma jaridar Daily trust takunkumi, dangane da wasu rahotanni na musamman da suka fitar, wanda ta baiyana a matsayin kara kanbama aiyukan ta’adanci da kuma fashin daji a kasar nan.
A cikin wasikar da kungiyar ta fitar mai dauke da kwanan wata 30 ga watan da muke ciki, mai dauke dasa hannun mataimakin daraktanta Kolawole Oluwadare, Ta baiyana cewa alhakin daya rataya ne akan wuyan kafafen yada labarai sanar da al’umma abubuwa masu muhimmanci.
Kungiyar ta SERAP, Tace a maimakon hukunta kafofin yada labarai, kan yin abunda al’umma zasu samu damar baiyana ra’ayoyinsu, kamata yayi gwamnatin taraiyya ta mayar da hankalinta wajen tabbatar da tsaro ga al’ummar kasa.