kungiyar nan mai rajin tabbatar da adalci a hukumomi da ma’aikatun gwamnati SERAP, ke yin kira ga bankin duniya da ya dakatar da baiwa jihohin kasar nan 36 lamuni, saboda zargin karkatar da kudaden da suke yi
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar lahadi.
Wasikar mai dauke da kwananann wata 25 ga watan da muke ciki, ta bukaci bankin duniya da ya gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudin da ya bayar a matsayin bashi da gwamnonin kasar nan suka karbo daga hannunsa, sannan ya dena bayar da bashin matukar ya gano akwai lauje cikin nadi a bada bashin.
Kungiyar ta ce akwai bukatar bankin duniyar ya dena baiwa jihohi bashi har sai sunyi cikakken bayani na gamsarwa kan yadda suka kashe sauran basussukan da suka karba daga wajensa.