kungiyar Kare muradan yan kabilar Igbo, ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana kwarin gwiwar cewa za a iya sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu kafin karshen shekarar 2023.
Hakan ya biyo bayan tattaunawar sirri da ake yi tsakanin kungiyar da hukumomin da abin ya shafa, a cewar wata sanarwa da babban sakatare kungiyar, Okechukwu Isiguzoro ya sanyawa hannu a ranar Lahadi.
Sakamakon haka, sanarwar ta bukaci dukkan masu fafutukar kafa kasar Biafra da su daina tada kayar baya ga Gwamnatin Tarayya na tsawon kwanaki 40, daga ranar 31 ga watan Oktoba, a matsayin wani bangare na sharudan sakin Kanu.
Sanarwar ta kara da cewa sakin Kanu zai zama abin mamaki ga al’ummar Kudu-maso-Gabashin Kasar nan, tare da yin kira ga ‘yan Nijeriya da Kanu ya yi wa laifi da su rungumi shirin afuwa da kuma maslahar Nijeriya.