Kungiyar Kwadago ta NLC ta gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya kuntatawa ‘yan Najeriya biyo bayan kalamansa da ya yi kan cire tallafin man fetur, wanda hakan ya fara haifar da matsalar karancinsa a yanzu haka.
A wata sanarwa da shugabanta, Comrade Joe Ajaero ya fitar, Kungiyar ta baiyana damuwarta kan yadda kalaman suka wasu masu gidajen mai suka rufe gidajen mansu, wanda hakan ya haifar da tashin farashin man.
Kazalika ya bayyana matakin ba tare da an tuntubi juna ba a matsayin abunda bai dace ba, Shugaban kungiyar ta NLC ya ce lamarin ya jefa jama’a r kasar nan cikin rashin jin dadi, a maimakon fatan da suke dashi ga sabuwar gwamnati.
A saboda haka,kungiyar kwadagon ta shawarci Tinubu da ya sake yin tunani kan manufofinsa na inganta tattalin arziki, domin temakawa jama’ar kasa, maimakon jefa su cikin halin tasku.