Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta yi kira ga rundunar yansandan jihar Naija data gagaguta zukole mutanen da datse hannayen wani karamin yaro dan shekara 12 a duniya.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Ba’dejo ne ya yi wannan kira a lokacin da ya ziyarci yaron dake kwance a babban Asibitin Karamar hukumar Lapai ta jihar Naija a jiya.
Ba’dejo ya yi kira ga ‘yan sanda da gwamnatin jihar data gaggauta yin bincike kan cin zalin da aka yiwa yaron tare da zakulo wadanda suka aikata danyen aikin.
A baya kakakin rundunar yansandan jihar Naija DSP Abiodun Wasiu ya tabbatar da cewar wasu mutane da ba’a san ko su waye ba, sune suka farwa yaron tare da sare masa hannayensa a lokacin da shanunsa ke kiwo a kauyen Mayaki dake karamar hukumar Lapai.